in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yara miliyan 11 ne hadarin El Nino ke yiwa rayuwar su barazana a gabashi da kudancin Afrika, in ji hukumar UNICEF
2015-11-12 11:51:40 cri
Hukumar kula da lafiyar kananan yara ta MDD wato UNICEF, ta yi gargadin cewar sakamakon hadarin El Nino, matsaloli irin su ambaliyar ruwa da tsagewar kasa da cutuka zasu iya haifar da matsalolin da zasu iya yin barazana ga lafiyar kananan yara sama da miliyan 11 a gabashi da kudancin Afrika.

UNICEF, ta fadi hakan ne a wani rahoton ta, wanda ya shafi hasashen yanayi, wanda ya yi nazari dangane da irin matsalolin da karuwar sauyin yanayin wato El Nino zasu iya haifarwa ta fuskar karancin abinci mai gina jiki da harkar ilmi da kula da lafiya.

Rahoton ya nuna cewar matsalar za ta iya shafar al'ummomi dake zuwa a nan gaba, sai dai idan al'ummomim da abun ya shafa suka samu wadatar tsabtattacen ruwan sha, da abinci mai gina jiki ga kananan yara, wanda zai basu kariya daga fuskantar barazanar kamuwa daga cutuka.

Hadarin El Nino ya kan afkuwa ne lokaci bayan lokaci, wanda ke shafar kananan yara, kuma a shekarun 2014 da 2015, matsalar ta faru ne sakamakon yadda kananan yara da iyayen su ke dogara kacokan kan abinci da ake basu a matsayin tallafi daga sauran kasashen duniya.

Rahoton na UNICEF, ya kara da cewar, matsalar ta fi shafar al'umma marasa wadata inda take haddasa musu cutuka a wasu lokutan har ma da rasa rayuka.

Baya ga wadancan matsaloli, a cewar UNICEF, matsalar ta El Nino na haifar da cutuka irin su cutar zazzabin cizon sauro da cutar gudawa da sauran cutukan da ke saurin hallaka kananan yara.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China