Shugaba Zuma wanda ya bayyana hakan a ranar Jumma'a gabanin komawarsa gida, bayan halartar taron cika shekaru 70 da cimma nasarar yakin kin harin Japanawa da ya gudana a nan birnin Beijing, ya kara da cewa kasarsa za ta karbi bakuncin wannan taro mai muhimmanci a matsayinta na daya daga shugabannin taron na FOCAC, wanda ake fatan zai samu halartar shugabannin nahiyar Afirka, da shugabannin hukumomin kasa da kasa da na shiyya-shiyya.
Ya ce Sin da nahiyar Afirka na da alaka mai fadi, kuma yanzu lokaci ya yi da sassan biyu za su kara inganta gajiyar da suke ci daga juna, ta fuskar bunkasa masana'antu, da samar da ababen more rayuwa.
Wannan dai taro da Afirka ta Kudu za ta karbi bakunci shi ne na irin sa na farko da zai gudana a nahiyar Afirka. (Saminu Hassan)