Kafofin watsa labarai na kasar sun rawaito cewa rundunar Najeriya ta yi amfani da sojin haya a ci gaban yakin da take da mayakan kungiyar Boko Haram.
Da yake maida martani kan wadannan rahotanni, kanal Rabe Abubakar, kakakin rundunar sojojin Najeriya, ya bayyana cewa zarge-zargen wadannan kafofi ba su da tushe balantana gaskiya, kuma wani yunkuri ne na shafa wa rundunar sojojin Najeriya kashin kaji.
Mista Abubakar ya nuna cewa wannan kamfe na da manufar lalata kokarin da sojojin Najeriya suke yi da ma sauran hukumomin tsaro dake aiki tukuru domin murkushe mayakan kungiyar dake arewa maso gabashi.
Kakakin ya bayyana cewa rundunar na da isassun sojoji da ta baiwa horo domin yaki da 'yan ta'adda a arewa maso gabashin Najeriya, ba sai ta nemi taimakon sojin haya ba.
A cewarsa, rundunar Najeriya ta kyautata dakarunta sosai, sannan kuma tura sabbin kayayyaki tun farkon kama aikin sabon shugaban kasar, kuma ba ta bukatar sojin haya, ko a cikin gida ko daga waje, domin kawo karshen mayakan kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar bisa lokacin da aka tsaida.
Haka kuma ya bayyana cewa, dakarun Najeriya suna iyakacin kokarinsu domin kawo karshen wannan matsala cikin gajeren lokaci, ta 'yan ta'adda da ma sauran kungiyoyi masu aikata manyan laifuka dake arewa maso gabashin kasar. (Maman Ada)