Babban darektan hukumar raya harkokin sadarwa na zamani na Najeriya(NITDA) Peter Jack wanda ya yi wannan kiran a birnin Legas, cibiyar kasuwancin Najeriya. Ya bayyana cewa, zuba jari a wannan sashe zai taimaka wajen bunkasa kasa, baya ga ribar da za a girba nan da nan kan jarin da aka zuba.
Peter Jack ya yi kira ga masu zuba jari daga ketare da su hanzarta cin gajiyar damammakin harkar zuba jari a bangaren sadarwa na zamani a Najeriya. Ya kuma shaidawa manema labarai cewa, a wannan shekara hukumarsa ta shigo da wasu cibiyoyin sadarwa na zamani guda 14 cikin kasar baya ga wasu fitattun kamfanoni da ke cikin kasar da suka baje kolin hidimomin da suke bayarwa ga duniya.
Sashen sadarwa na zamani dai ya taimaka wajen ninka alkaluman GDP na kasar a cikin shekaru biyar din da suka gabata daga kashi 4.5 cikin 100 zuwa kashi 10 cikin 100. Akwai kuma alamun da ke nuna cewa, sashen zai kara bayar da gudummawa ga tattalin arzikin kasar.(Ibrahim)