in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
FIFA ta bayyana tsarin gudanar gasar Olympic ta birnin Rio
2015-11-11 14:44:30 cri
Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta zayyana yadda gasar Olympic ta birnin Rio dake tafe a shekarar badi za ta gudana.

FIFA ta ce za a bude gasar ne a birnin Brasilia a ranar 4 ga watan Agustan shekarar ta 2016. Za kuma a karkare gasar a ranar 20 ga watan na Agusta a filin wasa na Maracana, yayin da kuma mai masaukin baki wato kasar Brazil za ta buga wasannin ta ajin maza a biranen Brasilia and Salvador. Sauran biranen da za su dauki bakuncin wasannin na ajin maza da mata sun hada da Belo Horizonte, da Manaus da kuma Sao Paulo.

A bangare mata kuwa, za a bude wasannin ne ranar 3 ga watan Agustar shekarar 2016 a birnin Rio de Janeiro, a kuma kammala a ranar 19 ga watan a filin wasa na Maracana.

Tuni dai kasashe 9 suka samu gurbin shiga a dama da su cikin kasashe 16 da za su fafata a gasar wasannin na Olympic ajin maza, kasashen dai sun hada da Brazil, da Argentina, da Jamus, da kuma Denmark. Sauran su ne Sweden, da Portugal, da Fiji, da Mexico da kuma Honduras.

A bangaren mata kuwa, kungiyoyin kasashe 6 da suka samu gurbi a gasar sun hada da Brazil, da Colombia, da Germany. Sai kuma Faransa, da Afirka ta kudu da kuma Zimbabwe. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China