A wata sanarwar da CAVB ta fitar a Litinin din nan, ta ce Congo Brazzaville za ta karbin bakuncin wasan da ake sa ran gudanarwa tsakanin ranakun 7 zuwa 14 ga watan Janairun shekara mai zuwa.
Brazzaville, ta taba karbar bakuncin gasar wasanni ta Africa a watan Satumba, a don haka CAVB ta ce ta gamsu da ingancin kayayyakin aikin da kasar ke da su na karbar bakuncin gasar wasannin.
Dama dai CAVB ta ayyana cewar, za ta zabi kasa guda ne daga Afrika don karbi bakuncin wasannin, kuma kungiyar wasan raga ta kasar Kenya ta sha zawarcin karbar bakuncin wasan, amma daga bisani Brazzaville ta yi nasarar karbar bakuncin gasar.
Kasashen da suka yi rajistar fafatawa a gasar sun hada da Algeria, da Tunisia, da Gambia, da Cape Verde, da Mali, da Burkina Faso, da Najeriya.
Sauran su ne Ghana, da Central Africa, da Congo Brazzaville, da Congo RDC, da Cameroon, da Gabon, da Kenya, da Masar, da Sudan, da Uganda, da Angola, da Mozambique, da Zimbabwe, da Botswana, da kuma Madagascar. (Ahmad Fagam)