in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Infantino zai kauracewa takara a zaben FIFA idan har Platini ya tsaya
2015-11-11 14:50:51 cri
Babban sakataren hukumar UEFA Gianni Infantino, ya fada a Talatar nan cewar, zai hakura da tsayawa takarar shugabancin hukumar FIFA, matukar shugaban UEFA Michel Platini ya tsaya takarar neman shugabancin hukumar ta FIFA.

Shugaban na UEFA wanda a halin yanzu yake amsa tuhuma, sannan aka kore shi daga dukkanin al'amurran da suka shafi kwallon kafa, a yanzu an ba shi damar tsayawa takarar.

Infantino, ya shedawa mujallar wasanni ta Italian cewar, Platini dai shugaban sa ne, kuma ya yi aiki tare da shi na tsawon shekaru 9. Kuma a bayyane take karara yana samun goyon baya daga gare shi, matukar dai zai tsaya takarar to shi kan ya hakura.

Ya ce ba zai taba yin takara da Michel ba idan har zai tsaya, to shi zai janye. Kuma wannan tamkar yin biyayya ne. Ya ce amma a halin yanzu, shi ne dan takara da yake samun goyon baya 100 bisa 100, bama daga yankin turai ba, har ma daga dukkanin bangarorin wasannin kwallon kafa na duniya baki daya.

Masu bincike daga kasar Swiss na tuhumar Platini ne tun a watan Satumba saboda biyan kudin frances na kasar Swiss miliyan 2 kwatankwacin dalar Amurka million 2 wanda ya karba daga hukumar ta FIFA a shekarar 2011, lamarin da ya sa aka dakatar da shi daga al'amurran kwallon kafa har na tsawon watannin 3.

Kimanin 'yan takara 7 ne zasu fafata domin maye gurbin tsohon shugaban FIFA Sepp Blatter, zaben wanda ake sa ran gudanarwa a ranar 26 ga watan Fabrairun shekara mai zuwa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China