A ranar alhamis ne dai manyan jami'ai daga Amurka,Rasha,Saudia da Turkiya suka hadu a tattaunawa karo na farko a Vienna don tatauna yadda za'a warware matsalar da Syrian ke fuskanta.
Mataimakin Ministan harkokin wajen kasar Sin Li Baodong ya halarci zaman tattaunawar na musamman da aka kira na yau jumma'an a Vienna wanda ya hada dukkannin jami'an diflomasiya daga kasashen da dama da suka hada da Iran.
Kasar Sin dai ta dade tana maida hankalin ta a yanayin siyasar da kasar Syria ta tsinci kanta a ciki inda take bada goyon bayan tattaunawa kamar yadda sauran kasashen duniya suke yi, inji Kakakin Lu Kang.