Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan yayin taron kungiyar kula da harkokin kudi da tattalin arziki ta kwamitin tsakiya na JKS, ya ce, za a yi amfani da manufofi da nagartattun tsare-tsaren harkokin kudi yayin da ake kokarin samar da yanayin gyare-gyaren tattalin arzikin da ya dace a cikin gida.
Shugaba Xi ya kuma bayyana cewa, kamata ya yi gwamnati ta bullo da manufofin da suka dace ga harkokin masana'antu ta yadda za su tallafawa tsarin tattalin arzikin kasar tare da inganta yanayin kasuwannin da za su taka muhimmiyar rawa a bangaren masu sayen kayayyaki.
Bugu da kari, shugaban ya ce kamata ya yi gwamnati ta mayar da hankali wajen rage matsalar yawan kayayakin da masana'antu ke samarwa, da rage kudaden tafiyar da kamfanoni da cunkuson kasuwannin sayar da gidaje tare da gina kasuwar hada-hadar kudi mai inganci da kuma kare 'yancin masu zuba jari. (Ibrahim Yaya)