Kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Peru ta sanar a ranar Talata cewa, ta sanya tsohon dan wasan gaban kulob din Bayern Munich Paolo Guerrero cikin jerin 'yan wasanta don share fagen wasannin da kungiyar za ta buga da Paraguay da Brazil a wata mai zuwa don neman izinin halartar zagayen karshe na gasar cin kofin duniya mai zuwa.
Guerrero mai shekaru 31 a duniya zai hada kai da Claudio Pizarro na kulob din Werder Bremen, da Yordy Reyna na kulob din Red Bull Salzburg, wajen jagorantar kai hari ga gidajen abokan karawarsu.(Bello Wang)