Wannan ne karo na farko da 'yar wasa Fan Yilin mai shekaru 15 kacal da haihuwa, ta halarci gasar wasan gymnastics ta duniya, kana ita ce 'yan wasa ta farko da ta samu maki 15.366 a wasan.
Bayan ita, 'yar wasan kasar Rasha Komova Viktoriia, da abokiyarta Spiridonova Daria, da kuma 'yar wasa daga kasar Amurka Kocian Madison, su ma suka samu maki 15.366. Don haka, dukkanin 'yan wasan hudu wadanda suka samu maki daya wato 15.366 suka zama zakarun wasan tare. Hakan ya sa aka soke lambar azurfa da ta tagulla a wasan.(Zainab)