Sai dai babban kocin kungiyar Gerardo Martino bai samu damar samun Lionel Messi da Sergio Aguero ba, domin dukkansu na cikin murmurewa daga raunukan da suka ji masu tsanani.
Da ma Higuain ya daina taka leda cikin kungiyar Argentina bayan da kungiyar Chile ta doke Argentina bisa bugun daga kai sai mai tsaron gida a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Amurka da ya gudana a watan Yunin da ya gabata.
Higuain mai shekaru 27 da haihuwa ya taba jefa kwallaye 9 cikin raga yayin da kungiyar Argentina ke neman shiga zagayen karshe na gasar cin kofin duniya a wancan karon. Haka kuma ya taka rawar gani a wasanni 8 da ya buga a wannan kakar wasa cikin kulob din Napoli, inda ya samu buga kwallaye 7 cikin raga.
Wasu 'yan wasan kungiyar Argentina wadanda suka farfado daga raunukan da suka ji su ma yanzu haka sun koma kungiyar su, 'yan wasan da suka hada da Marcos Rojo, Ever Banega da Enzo Perez.
A halin yanzu kungiyar Argentina wadda ta taba lashe kofin duniya sau 2 ta kasance ta 7 a teburin wasannin a yankin latin Amurka, ganin yadda ta samu maki daya kawai bayan wasanni 2 da ta buga da Ecuador da Paraguay.
Kungiyar za ta kara da Brazil a birnin Buenos Aires a ranar 12 ga watan Nuwamba, sa'an nan bayan wasu kwanaki 5 za ta buga wasa da Colombia a Barranquilla.(Bello Wang)