Sharhin ya bayyana cewa, a tsakiyar watan Nuwanba, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai tashi zuwa birnin Antalya dake kasar Turkiya, domin halartar taron koli karo na 10 na G20.
Kungiyar G20 tana shafar rayuwar kashi 2 cikin 3 na al'ummar duniya, wadanda yawan tattalin arzikin su ya kai ga kashi 90 cikin dari na al'ummar duniya. Kaza lika cinikayyar wannan kaso ta kai kashi 80 cikin dari na al'ummar duniya. Tana kuma kunshe da manyan kasashe masu ci gaba, da sabbin kasashen da suka fi samun bunkasuwar tattalin arziki a duniya, ta kuma kasance tsarin hadin gwiwar tattalin arziki a tsakanin kasa da kasa na farko, mai kunshe da kasashe masu ci gaba, da kasashe masu tasowa suka shiga, inda suke tsaida kuduri cikin adalci. Don haka kungiyar G20 ke taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya. (Zainab)