Mr. Zhu wanda ya bayyana hakan a jiya Jumma'a, bayan da ya halarci taron mataimakan ministocin kudi, da na shugabannin manyan bankunan kasashen kungiyar G20 da ya gudana a birnin Istanbul na kasar Turkiya, ya bayyana wa 'yan jarida cewa, kasar Australia ce ta jagoranci kungiyar G20 a bana, yayin da Turkiya za ta jagoranci kungiyar a badi, sai kuma kasar Sin da za ta jagoranci G20n a shekarar 2016.
A sabili da haka ne a cewarsa, kasashen uku, za su taka muhimmiyar rawa, wajen tsara ayyukan kungiyar, wadanda zasu kyautata tsarin ta, da kuma sa kaimi ga dauwamammen ci gaban tattalin arzikin duniya.
Ya yin taron na yini 2, wakilai mahalarta sun nuna sha'awarsu ga tsarin tattalin arzikin Sin. Game da hakan Mr. Zhu ya ce tattalin arzikin Sin yana bunkasa cikin sauri, yana kuma sahun gaba a duniya baki daya. Ya ce a bana, Sin ta ba da gudummawa mai yawa ga bunkasa tattalin arzikin duniya, da kason da ya kai 27.8 cikin dari, yayin da Amurka ta ba da gudummawar kaso 15.3 cikin dari. Wanda hakan ke nuna cewa kasashen Sin da Amurka, sune kan gaba wajen bada gudummawar bunkasa tattalin arzikin duniya baki daya.(Fatima)