Sanarwar ta kuma bayyana cewa, koda yake wasu daga muhimman kasashe masu saurin ci gaba a fannin tattalin arziki sun riga sun bunkasa, a yanzu haka kuma tattalin arzikin duniya na farfadowa sannu a hankali, duk da rashin daidaito da ake samu tsakanin yankuna daban daban a fannin bunkasuwar tattalin arziki.
Har wa yau sanarwar ta ce kawo yanzu ba a kaiga biyan bukatun al'ummar duniya wajen samar da aikin yi ba, kana akwai hadari da kasuwar hada-hadar kudade ke fuskanta, da ma batun matsalolin siyasa tsakanin kasashe daban daban, da dai sauran batutuwa.
Bugu da kari sanarwar ta bayyana alkawarin da shugabannin kasashe membobin kungiyar ta G20 suka yi, na kara yin hadin gwiwa tsakaninsu don sa kaimi ga samun bunkasuwar tattalin arziki. A daya hannun kuma, a bana kungiyar G20n ta tsara shirin kara yawan GDP na dukkan kasashe membobinta da kashi 2 cikin dari nan da shekaru biyar masu zuwa.
A gun taron kolin, shugabannin sun amince da kudurin gina ababen more rayuwa a sassan fadin duniya, ta yadda hakan zai sa kaimi ga hukumomin kasashe, da hukumomi masu zaman kansu, wajen kara zuba jari ga ayyukan more rayuwa.
Kana sanarwar ta nuna cewa, kara tabbatar da bunkasar tattalin arzikin duniya, da kasuwar hada-hadar kudi za su taimakawa, wajen samun bunkasuwa mai dorewa.
Sanarwar ta kara da cewa, shugabannin sun dauki matakai da dama, don tabbatar da adalci kan tsarin biyan haraji, da kara sa ido kan aikin biyan harajin, da yaki da laifin zambar biyan haraji. Baya ga amincewa da wani shirin yaki da cin hanci da rashawa.
Bugu da kari sanarwar ta bayyana hadin gwiwa a fannin makamashi, a matsayin aikin da aka aiwatar tun da farko, yayin da kuma ake kara maida hankali kan sauyin yanayi, da batun kalubalen yaki da cutar Ebola da dai sauransu. (Zainab)