in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fitar da Arsenal da Chelsea daga gasar cin kofin League Cup
2015-10-29 13:31:35 cri
Dukkan kuloflikan Arsenal da Chelsea sun kasa samun nasara a zagaye na 4 na wasannin gasar cin kofin English League Cup wadanda suka gudana a ranar Talata.

A wancan rana, Sheffield Wednesday ta doke Arsenal da ci 3 da nema, yayin da Stoke ta yi galaba kan Chelsea da ci 6 da 5, bisa bugun daga kai sai mai tsaron gida.

A bangaren Sheffield Wednesday, 'yan wasanta Ross Wallace, Lucas Joao da Sam Hutchinson ne suka samu maki, ta yadda aka sanya kungiyar cikin zagayen kusa da na karshe na gasar mafi girma na biyu tsakanin kuloflikan kasar Birtaniya.

Yayin da Arsenal, wacce ke kan gaba a teburin gasar Premier League tare da Manchester City, a wannan wasa ta rasa Alex Oxlade-Chamberlain, da Theo Walcott, wadanda suka ji rauni cikin mintuna 20 bayan da aka fara wasan.

A wasan da aka buga tsakanin Stoke da Chelsea, Jonathan Walters na bangaren Stoke ya zara kwallo guda a raga sannan bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Loic Remy ya kubutar da Chelsea yayin da zara kwallo guda a wasan karin lokaci.

Daga bisani a matakin bugun daga kai sai mai tsaron gida, 'yan wasa 9 sun samu nasarar zara kwallaye a raga daya bayan daya, amma kwallo ta karshe da Eden Hazard na Chelsea ya buga ya kasa shiga cikin raga, ta haka aka kori Chelsea daga gasar ta cin kofin English League Cup.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China