in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu mutane 8 sun nemi shugabancin hukumar FIFA
2015-10-29 13:30:32 cri
A kokarin share fagen kada kuri'a don zaben shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta duniya FIFA, wasu mutane 8 sun nuna aniyar su ta takarar neman samun mukamin a ranar Litinin 26 ga wata. Mutanen sun hada da PRINCE ALI BIN AL HUSSEIN, mamba a kwamitin zartaswa na hukumar FIFA. Mutumin mai shekaru 39 a duniya ya taba takara da Sepp Blatter don neman samun kujerar shugabancin FIFA a bana. A koda yaushe yana kokarin yin kiran cewa, ya kamata a bayyana karin ayyukan hukumar FIFA a gaban idanun jama'a, haka kuma ya dau alkawarin mayar da karin kudi ga hukumomin wasan kwallon kafa na kasashe daban daban.

Ban da haka kuma, sai MICHEL PLATINI, shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta nahiyar Turai UEFA, shi ma ya kasance cikin mutanen 8 masu neman shugabancin hukumar FIFA. MICHEL PLATINI ya taba jagorantar kungiyar kula da gasar cin kofin duniya da ta gudana a kasar Faransa a shekarar 1998, haka kuma an tsawaita wa'adin aikinsa a matsayin shugaban hukumar UEFA har sau biyu. Sai dai an taba dakatar dashi daga mukaminsa na kwanaki 90 yayin da aka gudanar da bincike kan yadda UEFA a karkashin jagorancinsa ta biya wa wasu mutane kudi EURO miliyan 1.8, ba tare da sa hannu kan wata kwangila ba.

Dayan daga cikin mutane 8 masu takarar kujerar shugabancin hukumar FIFA shi ne JEROME CHAMPAGNE, tsohon mataimakin sakatare janar na hukumar FIFA. Shi ma ya taba takara da mista Blatter a bana, amma bai samu nasara ba sakamakon yadda ya kasa samun amincewar hukumomin wasan kwallon kafa na wasu kasashe ko yankuna 5, wanda ya kasance cikin sharrudan da aka gindaya wa masu takarar shugabancin hukumar FIFA.

A nashi bangaren DAVID NAKHID, tsohon kyaftin din kungiyar kasar Trinidad da Tobagao, shi ma yana cikin masu takarar zama shugaban FIFA. Ya taba buga kwallo a kasashen Switzerland, Belgium, da kasar Amurka. Yayin da gudunmowa mafi girma da ya samar a fannin wasan kwallon kafa shine kafa wasu makarantun koyar da fasahar wasan kwallon kafa da yayi a kasar sa.

Sauran masu takarar samun shugabancin hukumar FIFA sun hada da TOKYO SEXWALE, wani dan kasar Afirka ta Kudu, wanda ya taba gwagwarmayar yakar ra'ayin nuna bambancin launin fata tare da Nelson Mandela. Ya kasance mamba a kwamitin hulda da kafofin yada labaru na hukumar FIFA, da mamba a kwamatin karbar bakuncin gasar cin kofin duniya a kasar Afirka ta Kudu a shekarar 2010.

Sauran masu neman zama shugaban hukumar FIFA sun hada da SHAIKH SALMAN BIN BRAHIM AL KHALIFA, shugaban hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafa ta nahiyar Asiya, da GIANNI INFANTINO, sakatare janar na hukumar UEFA, gami da MUSA BILITY, shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta kasar Laberiya.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China