in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaro na MDD ya yi maraba da nada Sidikou a matsayin wakilin musamman kan batun DRC
2015-11-10 09:44:07 cri
A ranar Litinin din nan kwamitin sulhu na MDD ya yi maraba da nadin da aka yi ma Maman Sidikou a matsayin wakilin musamman na Magatakardar MDD a jamhuriyar demokradiya ta Kongo.

A cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin ya fitare an ce Sidikou har ila yau shi ne zai jagoranci ofishin daidaita ayyuka na majalissar wato MONUSCO, don haka kwamitin ke tabbatar mashi da dukkan goyon baya yadda ya kamata.

Kwamitin tsaron mai mambobi 15 ya kuma yaba ma wanda ya bar kujeran a yanzu Martin Kobler bisa ga iyakacin kokarin da ya yi da kuma gaggarumin gudunmuwar da ya bayar a cikin shekaru 2 wajen goyon bayan aiwatar da shirin MONUSCO.

Kwamitin ya yaba bisa ga wassu cigaban da aka samu kan yanayin tsaro a gabashin kasar cikin shekaru 14, amma kuma yana nuna damuwa a kan karuwar tabarbarewar tsaron da halin jin kai sakamakon rashin daidaito na kungiyoyin 'yan ta'adda na cikin gida da kasashen waje. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China