Mukaddashin mataimakin kakakin MDD Farhan Haq ne ya rawaito wannan tsokaci na Mr. Kobler, yayin taron ganawa da 'yan jarida na rana rana da ya gabata a ranar Laraba.
Wata sanarwa daga rundunar ta MONUSCO dai ta bayyana cewa, an harbe ma'aikacin ne a hanyarsa ta zuwa wurin aiki da sanyin safiyar ranar Larabar, a birnin Beni dake yankin Arewa maso Gabashin kasar ta Congo, yankin da ke ci gaba da fama da yawan tashe tashen hankula. (Saminu Alhassan)