Ofishin ya yanke shawarar hakan ne sakamakon babban hadarin da fararen hula ke fuskanta a yankin Goma-Sake dake arewacin Kivu, kamar yadda mataimakin kakakin majalissar Eduardo Del Buey ya yi bayani ma manema labarai.
A cikin bayanin Majalissar, ta ce tun tsakiyar watan Mayu, wannan yankin yake fuskantar hare hare daga wajen 'yan tawaye na M23 a kan sansanin sojojin kasar Kongo, abin da ke nuna cewa suna son kutsa kai a cikin garin na Goma da Sake.
A bayaninsa wannan hare hare na bayan bayan nan da aka fara shi daga ranar 14 ga watan Yulin nan, kungiyar 'yan tawayen sun yi amfani da manyan makamai inda suka bude wuta ba kakkautawa ta ko'ina, abin da ya yi sanadiyyar hasarar rayukan fararen hula da dama, kuma har ila yau harin ya shafi cibiyoyin MDD.(Fatimah Jibril)