in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu ya yi kiran da a aiwatar da yarjejeniyar MDD game da kasashen da ke yankunan na Great Lakes
2013-07-26 10:26:34 cri
A ranar Alhamis ne kwamitin sulhu na MDD, ya yi kiran da a aiwatar da yarjejeniyar MDD game da kasashen da ke yankunan na Great Lakes da ta cije, kana ya bukaci da a hanzarta kawo karshen rigingimu tsakanin 'yan tawaye da dakarun gwamnati a Jamhuriyar demokiradiyar Congo.

Kwamitin sulhun ya nanata goyon bayansa na ganin an aiwatar da yarjejeniyar karkashin shirin samar da zaman lafiya, tsaro da hadin kai a Jamhuriyar demokiradiyar Congo(DRC) da kuma yarjejeniyar shiyyar, wanda ke da muhimmanci wajen samar da zaman lafiya da tsaro mai dorewa a gabashin Congo da kuma yankunan na Great Lakes.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China