Nesirky ya ce babban darektan cibiyar abinci ta duniya (WFP) Ertharin Cousin ya yi kira ga masu dauke da makamai su tabbatar da cewa kungigoyin tallafawa bil adama sun samu damar taimakawa jama'a mabukata, kuma a duk inda suke a cikin kasar.
An samu dakatar da fada da ya sake barkewa ranar Lahadi tsakanin dakarun gwamnati da na kungiyar 'yan tawayen M23 a wajen garin Kanyaruchiya, mai nisan kusan kilomita 15 da Goma, babban birnin yankin arewacin Kivu, in ji hukumar kawo daidaito a Jamhuriyar Demokrdaiyar Congo ta MDD (MONUSCO).
Hukumar ta baiyana a cikin wani rahoto cewa koda yake kura ta lafa, har yanzu ana zaman dar-dar a Goma.
A yayin jawabi ga manema labarai da aka saba yi kullum, Nesirky ya ce Mr Cousin ya kai ziyara Congo DRC a wannan mako, inda ya kara jadadda cewa manufa daya ta hukumomin MDD da sauran abokan aikinsu daga cibiyoyi da ba na gwamnati ba shi ne samar da tallafin ceton rai ga jama'a mabukata. (Lami Ali)