Wakiliyar musamman ta magatakardan MDD a yankin Great Lakes na Afirka Mary Robinson tayi kira ga shugabanni a yankin da su ci gaba da aikin tabbatar da nasarar sabon shirin kafa zaman lafiya a Jamhuriyar Demokuradiyar Congo, in ji mai magana da yawun MDD Martin Nesirky yayin jawabi ga 'yan jarida.
Robinson ta yi wannan kira ne a kasar Burundi yayin ziyarar farko a yankin na Great Lakes, wanda ta fara ranar 29 ga watan Afrilu kuma za ta gama a karshe wannan mako, inji Martin Nesirky.
Wakiliyar ta gana da shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunzisa da kuma wakilan shirin kafa zaman lafiya a yankin Great Lakes na kungiyar hada kan kasashen Afirka da kuma na taron kasa da kasa kan yankin Great Lakes. Tayi kira ga shugabannin da su ci gaba da kokari a fuskar tabbatar da bukatar zaman lafiya a yankin.
Dangane da batun shirin zaman lafiya, tsaro da hadin gwiwa a Jamhuriyar demokuradiyar Congo da ma yankin baki daya, Robinson ta ce, an yi yarjejeniyoyi a baya, to amma ya kamata a wannan karo ya zamo daban sannan kuma a fara aiwatar da shirin yanzu.
A ranar Alhamis, Robinson ta tattauna da shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni dangane da aiwatar da yarjejeniyar da kasashe guda 11 suka rattaba hannu kanta a watan Fabrairun 2013 domin a samu kawo karshen rikice-rikice da fadace-fadace a gabashin Jamhuriyar Demokuradiyar Congo da kuma kafa zaman lafiya a yankin da aka dade ana fama da rikici.
Wakiliyar ta musamman ta jadadda cewa, ya dace a tabbatar cewa hadin kai a siyasance kan yarjejeniyar ita ce zata zamo madogara a yunkurin da ake na warware rikicin domin a cimma zaman lafiya, tsaro da kuma bunkasa. (Lami Ali)