in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya bukaci samar da karin tallafi ga al'ummu mafiya fama da talauci
2015-07-07 10:23:21 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya bukaci sassan masu ruwa da tsaki da su zage damtse, wajen samar da karin tallafin yaki da fatara, musamman ga al'ummu mafiya fama da talauci dake kasashe daban daban.

Mr. Ban wanda ya bayyana hakan a jiya Litinin, ya ce, duk da irin nasarorin da ake samu game da muradun karni, a hannu guda akwai bukatar daukar karin matakan tabbatar da cewa, ba a bar al'ummu mafiya talauci a baya ba.

Babban magatakardar MDDr ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da rahoton muradun karni na bana a birnin Oslon kasar Norway. Rahoton ya nuna irin tasirin da kudurorin cimma maradun karni suka yi, wajen yaki da talauci, tare da fidda miliyoyin al'ummun dake cikin matsanancin halin fatara daga kangin yunwa, tare da baiwa 'ya'ya mata damar samun ilimi yadda ya kamata.

Cikin jawabin da ya gabatar yayin kaddamar da rahoton, Mr. Ban ya ce, ya kamata nasarorin da aka cimma ya zuwa su faranta ran al'ummar duniya. A hannu guda kuma akwai bukatar mai da hankali ga wuraren da aka samu gibi domin daukar matakan gyara.

Ya ce, alkamu sun nuna irin yadda manufofin cimma muradun karni suka yi matukar tasiri ga hatta kasashe mafiya talauci, wajen samar da ci gaba cikin shekaru 15 da suka gabata. Don haka, a cewar Ban Ki-moon, kudurorin da za a sanya gaba bayan shekarar 2015 sun hada da tabbatar da dorewar kudurorin da aka cimma nasarar su, matakin da ake fatan amincewa da shi yayin babban taron watan Satumba mai zuwa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China