Daga cikin wadanda suka mutu, akwai farar hula guda da kananan 'yan mata biyu da suka tada boma boman da suke dauke da su, in ji wannan sanarwa.
Tsibirin Ngouboua, ya taba fama da irin wannan hari a ranar 13 ga watan Fabrairun shekarar 2015, da ya kasance hari na farko da kungiyar Boko Haram ta kai a kasar Chadi. Daga bangaren Chadi, an samu mutuwar soja guda da wani basarake, kana mutane da dama da suka jikkata.
A ranar 1 ga watan Nuwamba, wasu tagwayen hare hare biyu da aka kai kan wasu sansanonin sojan Chadi, a shiyyar tafkin Chadi sun yi sanadiyyar mutuwar soji uku da jikkata wasu 14.
A ranar 6 ga watan Oktoba, sojojin Chadi 11 suka mutu yayin da wasu 13 suka ji rauni a wani harin mayakan kungiyar Boko Haram da suka fito daga Najeriya. Bayan kwanaki hudu, wasu hare-haren ta'addanci sun halaka mutane 41 da jikkata 48 a kasuwar Baga Sola, birnin yankin tafkin Chadi guda, dake karbar 'yan gudun hijirar Najeriya da Nijar fiye da dubu 6. (Maman Ada)