Daga bangaren maharan, an kashe goma sha shida da raunana guda, in ji wannan sanarwa.
A wannan rana, 1 ga watan Nuwamba, da misalin karfe 4 da mintoci 47 bisa agogon N'Djamena, sansanin soja na Bohama ya fuskanci harin 'yan kunar bakin wake uku, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum guda da jikkata wasu goma daga bangaren sojojin Chadi. 'Yan kunar bakin waken uku sun mutu nan take a lokacin harin, in ji wannan sanarwa.
Haka kuma a daidai wannan lokaci, a cewar sanarwar, an kai hari kan wani karamin sansanin soja na Kaiga-Kindiria, inda sojojin Chadi biyu suka mutu yayin da aka jikkita hudu, sannan aka kashe maharan Boko Haram 14 da raunana guda. (Maman Ada)