Rahotanni sun ce an yanke wa mutanen 10 hukuncin kisa ne a ranar Juma'ar da ta gabata, bayan da kotu ta tabbatar musu da laifin mallakar makamai, da amfani da abubuwan dake haddasa cututtuka, da kuma amfani da boma-bomai da dai sauransu.
A yayin da ake gudanar da bincike kan mutanen, wadanda ake zargin, sun amsa laifin su, ciki hadda shirya hare-haren kunar bakin wake da aka kai a birnin N'Djamena tsakanin ranar 15 ga watan Yuni zuwa 11 ga watan Yulin bana, wadanda suka haddasa mutuwar mutane 67, yayin da mutane 182 suka jikkata, baya ga hasarar dukiyoyi da hare haren suka haifar.
Bisa kididdiga, an ce daga shekarar 2009 kawo yanzu, kungiyar Boko Haram ta hallaka mutane a kalla dubu 15.
A kuma watan Fabarairun bana, kasashen Nijeriya, da Kamaru, da Nijer, da Chadi da Benin, sun kafa wata rundunar sojojin hadin gwiwa mai kunshe da sojoji 8700, domin yaki da kungiyar ta Boko Haram. (Zainab)