A ranar 15 ga watan Junin shekarar 2015, wasu hare haren kunar bakin sun faru a wasu muhimman wurare na tsaro dake N'Djamena, babban birnin kasar Chadi.
Haka kuma, a ranar 11 ga watan Juli, an kai wani harin kunar bakin wake a wata kasuwa da ke tsakiyar N'Djamena.
A dunkule wadannan hare hare da kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin kai su sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 67 kuma goma daga cikinsu 'yan kunar bakin waken ne, yayin mutane 182 suka jikkata baya ga asarar dukiyoyin jama'a masu dimbin yawa, a cewar kotu a birnin N'Djamena.
A cewar wata dokar da 'yan majalisar dokokin Chadi suka cimma a ranar 30 ga watan Julin shekarar 2015 dake yanke hukunci mai tsanani ga wadanda suka aikata ko suka taimaka wajen gudanar da ayyukan ta'addanci, mutanen goma da ake tuhuma, wadanda suke samun kariya daga wasu lauyoyi da aka gabatar musu, za su iyar fuskantar hukuncin kisa.
Amma sakamakon rashin wata doka ta musammun a lokacin da aikata wadannan ayyuka, kuma dokar ba ta da tanadi na gaba, kotun bai samu damar rike shaida a cikin tanade tanade masu muhimmanci na doka mai lamba 34 ta ranar 5 ga watan Augustan shekarar 2015 dake shafar hukunta ayyukan ta'addanci, in ji Louapambe Mahouli Bruno, babban alkali na kotun kai kara ta birnin N'Djamena. (Maman Ada)