Sanarwar ta yi bayanin cewa, a ranar Jumma'a, aka kashe Welly Nzitonda, dan Pierra Claver, daya daga cikin masu fafutukar 'yancin dan adam a kasar, sakamakon kama shi da 'yan sanda suka yi a Bujumbura.
Mr. Ban ya jaddada muhimmancin da ke akwai ga gwamnatin kasar na Burundi na kare rayukan al'ummarta da tabbatar da ganin irin wannan tashin hankali da kisan gilla an daina shi.
Magatakardar na MDD har ila yau ya nanata cewa, ya kama a yi iyakacin kokarin samar da mafita a siyasance ma rikicin da ake fuskanta a kasar, sannan ya yi kira ga dukkannin masu ruwa da tsaki da suka hada da mahukuntar kasar, kungiyoyin masu zaman kansu da na 'yan adawa ko da 'yan kasa ko ma wadanda suke zaune a kasashen waje da su maida hankali kwarai na ganin an daina kalaman batanci. Ya ce ya kamata su jinginar da duk wani shiri na tashin hankali, su kuma aiwatar da ayyukan ganin yadda za'a tattauna samar da zaman lafiya a kasar dake gabashin Afrika.(Fatimah Jibril)