Afam Ezekude, babban darakta a hukumar hana satar basira ta kasar wanda ya bayyana hakan ya ce har ila yau tana shirya tarukan bita da samar da kafar wayewar da kan dalibai a makarantun sakandare game da hakan.
Mr. Ezekule ya shaida ma manema labarai cewa hukumar baya dokokin da ta kafa da hukuncin da ta kan yi ta kuma tsara wani shiri na musamman da zai wayar da kan jama'a game da illar aikata wannan laifi.
Daga cikin shirin a bayanin da ya yi akwai horas da dalibai a kan muhimmancin guje ma satar basira da ma kuma kare shi saboda ba da dadewa ba suna iya zama marubuta, masu kirkiro tare da mallakar basirar su.
Babban daraktan ya ce hukumar tana horas da manema labarai har ila yau game da yadda za su bayyana labarai a kan ayyukan da take yi a yaki da satar basira kuma tana tattaunawa da sarakunan gargajiya.
Ya ce jami'an hukumar suna cikin ayyukan da ake gudanarwa domin sa ido a kan masu aikata satar basira a manyan kasuwanin kasar da tituna domin kula da masu wannan danyen aiki. (Fatimah Jibril)