Mr. Lolo ya yi wannan kira ne a ranar Jumma'a, a jawabin da ya gabatar ga mahalarta taron. Ya ce batutuwan da suka jibanci cin hanci da rashawa, da ta'addanci, da sauyin yanayi, da karyewar farashin mai, na cikin ababen dake yiwa tattalin arzikin Najeriya dabaibayi. Don haka ya bukaci mahalarta taron da su himmatu, wajen gano hanyoyin da suka dace ta yadda za a maido da kimar kasar a idon duniya.
Kaza lika Mr. Lolo ya bayyana manufofin kasashen waje, a matsayin kari kan manufofin cikin gida, don haka taron tattaunawa game da manufofin zai shafi yadda kasar ke gudanar da tsare-tsarenta a ketare. Ya ce ya zama dole Najeriya ta zamo mai karfin gwiwa a halin matsi da yalwa, ta kuma dauki matakan duk da suka dace domin cimma nasarorin da ta sanya gaba. (Saminu Hassan)