Ministan tsaron kasar Karidjo Mahamadou, ya ce lamarin ya faru ne bayan da dakarun na Nijar suka bude wuta kan mayakan na Boko Haram wadanda ke dauke da ababan fashewa a lokacin da suke kokarin kutsawa garin na Diffa.
Ministan ya ce mayakan ba su cimma burin su ba kasancewar sojojin sun bude musu wuta ne kafin su kai ga daddasa boma boman, sai dai ba'a bayyana adadin mayakan Boko Haram da suka mutu ko suka jikka ko kuma aka kama su ba.
Mayakan Boko Haram sun yi wani shiri ne na tada boma bomai a dai dai lokacin rantsar da sabon gwamnan lardin Janar Abdou Kaza.
Kazalika, lamarin ya faru ne bayan gwamnatin Nijar ta ba da sanarwa a ranar 14 ga wannan wata na kara wa'adin dokar ta baci da kwanaki 15 a yankin na Diffa sakamakon samun yawaitar hare hare a yankin. (Ahmad)