A kalla mutane 41 suka mutu kana wasu 48 suka jikkata a ranar Asabar da yamma a cikin wasu hare haren boma bomai da kungiyar Boko Haram ta kai wata kasuwar birnin Baga Sola, dake yankin tafkin Chadi, a cewar wata sanarwa ta ministan sadarwa na kasar Chadi, Hassan Sylla Bakari. Daga cikin wadannan mutane da suka mutu, akwai 'yan kunar bakin wake su biyar da suke da namiji guda, mata biyu da kuma yara biyu. A halin yanzu kome ya lafa, kuma jami'an tsaro na aikinsu.
Gwamnatin Chadi ta bukaci mutanen kasar da su ci gaba da kasance cikin ko ta kwana kan wannan kungiya, da sojoji suke samun galaba kanta a fagen daga, dake amfani da mata da kananan yara domin kai hare haren ta'addanci, in ji mista Bakari. (Maman Ada)