A zagayen da ya gabata, kungiyar Guangzhou Evergrande Taobao ta yi kunen doki da kungiyar Shandong Luneng Taishan, wanda hakan ya hana ta damar zama zakara kafin rufe gasar. A zagayen karshe, ana bukatar ta kara samun maki daya, kafin ta kai ga zama zakara.
A karshe dai, kungiyar Guangzhou ta zamo zakara bayan cimma nasarar samun maki uku, bisa jimilla kungiyar ta tashi da maki 67, maki 2 sama da na kungiyar Shanghai SIPG.
A gun taron manema labaru da aka gudanar bayan gasar, mai horas da kungiyar Guangzhou Evergrande Taobao Luiz Felipe Scolari, ya jinjinawa 'yan kungiyar ta sa, yana mai cewa kungiyar Guangzhou Evergrande Taobao ta rasa nasara ne a wasa daya kacal a gasar ta CSL na wannan shekara, kuma babu shakka daukacin 'yan wasan na ta sun cancanci matukar yabo. (Zainab)