Mujallar Der Spiegel ta bayar da labari cewa, kwamitin neman daukar bakuncin gasar cin kofin duniya na kasa Jamus na wancan lokaci ya taba baiwa hukumar FIFA cin hanci da yawansu ya kai kudin Swiss Franc miliyan 10.3 don tabbatar da samun kuri'un goyon baya daga wakilai hudu daga nahiyar Asiya.
Ya kara da cewa a shekara ta 2002, shugaban hukumar FIFA na lokacin Sepp Blatter, ya zanta da shugaban kwamitin neman daukar bakuncin gasar cin kofin duniya na kasar Jamus Franz Beckenbauer, inda Balatter ya yi alkawarin samar da kudi Swiss Franc miliyan 250 don taimakawa kasar Jamus, wajen daukar bakuncin gasar cin kofin na duniya, amma da farko sharadi shi ne hukumar wasan kwallon kafa ta Jamus ta biya kudi Euro miliyan 6.7 ga hukumar FIFA tukuna. A lokacin Beckenbauer ya nuna aniyar sa ta bayar da wadannan kudade, amma mashawarcinsa ya ki amincewa. A karshe dai, tsohon shugaban kamfanin Adidas ya biya kudin.
Amma Niersbach bai bayyana dalilin hukumar wasan kwallon kafar kasar Jamus ba game da biyan wannan kudi, kana ya ce ya san wannan batu a yayin tattaunawar sa da Beckenbauer a 'yan kwanakin baya.
A halin yanzu, hukumar FIFA da hukumar wasan kwallon kafa ta Jamus suna gudanar da bincike kan wannan batu.(Zainab)