in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Alexandre Pato ya bayyana yiwuwar tsallakawa turai
2015-11-05 16:20:00 cri
Dan wasan gaban kungiyar kwallon kafan Corinthians ta Brazil, wanda ke bugawa Sao Paulo kwallo aro Alexandre Pato, ya tabbatar da aniyar sa ta sauya sheka zuwa daya daga kulaflikan Turai, bayan kammalar kakar wasanni ta bana. Dan wasan mai shekaru 26 da haihuwa, wanda kuma a baya ya taba taka leda a AC Milan na Italiya, a bana ya ciwa kungiyar Sao Paulo kwallaye 26 a wasanni 57 da ya buga, gabanin kammala zaman aro da yake yi a kulaf din na Sao Paulo.

Rahotanni na cewa manyan kulaflikan turai irin su Barcelona, da Arsenal, da Manchester United da kuma West Ham United na zawarcin dan wasan.

Pato wanda ya gana da manema labaru ranar Asabar bayan wasan su da Sport Recife, wanda aka tashi Sao Paulo na da kwallo 3 Sport Recife na nema, ya ce yana da kwantiragi a Corinthians ya zuwa karshen shekarar badi. Amma yana fatan amfani da damar musayar 'yan wasa ta watan Janairun farkon shekarar ta badi, domin komawa turai.

Ya ce abu ne mai wuya ya ci gaba da zama a Brazil, kuma koda yake bai san yadda za ta kaya game da wannan buri na sa ba, a hannu guda ya ce ya lashi takobin baiwa kungiyar Sao Paulo da yake bugawa kwallo dukkanin gudummawar da ta wajaba, ta yadda zai bar kungiyar cike da alfahari na irin gudummawar da ya bayar. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China