in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Neymar ya ciwa kungiyarsa ta Barcelona kwallaye hudu
2015-10-22 16:27:54 cri

A ranar 17 ga wata ne aka buga wasannin mako na 8 na gasar La Liga ta Spaniya,inda Cristiano Ronaldo ya zama dan wasan da ya fi zura kwallaye a tarihin kungiyar Real Madrid a wasan da kungiyarsa ta kara da Levante. Kuma Neymar ya ci kwallaye hudu a wasan da kungiyarsa ta Barcelona da fafata da Rayo Vallecano, Neymar ya taimakawa kungiyarsa wajen doke Rayo Vallecanon da ci 5 da 2. Wannan ne karo na farko da Neymar ya zura kwallaye hudu a raga a wasa daya tun lokacin da ya fara taka leda a kungiyar Barcelona.

Kafin a fara wasa tsakanin Real Madrid da Levante, dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ya nuna lambar yabo ta dan kwallon mafi fice a nahiyar Turai da ya lashe ga 'yan kallon da ke filin wasan. Kana a wasan ne, Ronaldo ya ci kwallon da ta ba shi damar zarce zarce RAÚL González Blanco wanda ya kasance dan wasa da ya fi zura kwallaye a tarihin kungiyar Real Madrid inda ya ci kwallaye 324 ya zuwa yanzu. Kuma a karshen wasan, Real Madrid ta doke Levante da ci 3 da nema.

A sakamakon raunin da dan wasan kungiyar Barcelona Leo Messi ke fama da shi a halin yanzu, Neymar da Luis Alberto Suarez sun taka leda tare a wasan da Barcelona ta yi da Rayo Vallecanon. A wasan, Neymar ya zura kwallaye hudu a raga, wannan ne karo na farko da Neymar ya ci kwallaye hudu a wasa daya tun lokacin da ya fara wasa a kungiyar Barcelona. A karshen wasan kungiyar Barcelona ta doke Rayo Vallecanon da ci 5 da 2. Kuma bayan wannan wasa, kungiyar Barcelona ta samu nasara a wasanni biyar a jere.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China