in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin Xi Jinping yana fatan kai ziyara kungiyar Manchester United bayan canja ziyarar da aka shirya zai kai kungiyar Manchester City
2015-10-22 16:27:18 cri
A wannan makon ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyara kasar Birtaniya, kuma daya daga cikin wuraren da aka shirya zai ziyarta shi ne kungiyar Manchester City. Amma bisa labarin da kafofin watsa labaru na Birtaniya suka bayar, an ce, hakika dai shugaba Xi Jinping yana son ya ziyarci kungiyar Manchester United, amma bangaren kasar Birtaniya ya tsara shugaba Xi Jinping zai je filin wasa na kungiyar Manchester City.

Bayanai na nuna cewa, a matsayinsa na mai sha'awar wasan kwallon kafa, shugaba Xi Jinping yana da burin kai ziyara filin wasa na Old Trafford, amma wannan bukata ta shugaba Xi ba ta samu ba, domin gwamnatin birnin Manchester ta tsara shugaba Xi Jinping zai ziyarci Man City ne maimakon Manchester United.

Jaridar Sunday Sun ta bayar da labarin cewa, magajin garin birnin Manchester shi ma mai sha'awar kungiyar Manchester City ne, don haka ya shirya shugaba Xi Jinping ya ziyarci kungiyar Manchester City. Kana babban jami'in gudanarwa na birnin shi ma ya goyi bayan wannan shiri, domin shi ma mai sha'awar kungiyar Manchester City ne.

Jaridar daily Mirrow ta bayar da labari cewa, manyan jami'an gwamnatin birnin Manchester da ke bayan kungiyar Manchester City suna sane da cewa, ziyarar shugaba Xi Jinping za ta kawo babban tasiri ga kungiyar Man City, don haka suke son ya ziyarci kungiyar ta yadda za ta samu moriya, amma ba Manchester United ba.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China