Wasan wanda ya samu halartar dunbun jama'a a filin wasa na Nakivubo, kuma mai masaukin bakin ta sha kashi ne da ci biyu da nema bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, kuma 'yan wasan Uganda Frank Kalanda da skipper Farouk Miya ne suka zara kwallayen.
A yayin da dan wasan Uganda Kalanda ya kai wani zazzafan hari, duk da cewar mai tsaron ragar Sudan Yassein Yousif Maki ya yi kokarin barar da kwallo, amma bayan mintuna 15 da wancan farmakin, yayi nasarar zara kwallon, yayin da shima Miya ya zara kwallo ta biyu a ragar Sudan bayan mintuna 35.
Dan wasan Sudan Mudather Eltaib, ya sha kai farmaki a Uganda amma masu tsaron gidan Uganda sun dakile aniyar tasa bai samu damar cimma burinsa ba.
Bayan hutun rabin lokaci an sauya mai tsaron gidan Sudan Hassan Wasswa Dazo.
Mai tsaron ragar Uganda James Alitho, ya yi nasarar hana kwallon shiga ragar a wani bugun daga kai sai mai tsaron raga wanda Eltaib na Sudan ya buga.
Sudan sun sha kai zafafan hare hare, amma 'yan wasan na Uganda basu sassauta musu ba.
'yan wasan Uganda Samson Ceaser Okhuti da Tony Odur sun zubar da kwallaye masu yawa ga kungiyar tasu.
Za'a gudanar da zagaye na biyu na wasan a Khartum a ranar 24 ga wannan watan, inda za'a daddale ko Uganda zata yi nasara ko a'a, idan har ta tsallake zata samu damar shiga gasar cin kofin nahiyar Afrikan wanda za'a gudanar a kasar Ruwanda tsakanin watannin Janairu zuwa Fabrairun shekara mai zuwa.(Ahmad)