Cikin jawabinsa, Ban Ki-moon ya bayyana cewa, a halin yanzu, babu wata kasa ko kungiya da ta iya tinkarar kalubaloli ko rikici da kanta ita kadai, MDD wadda ta riga ta kasance a nan duniya har shekaru 70 ta iya kasance mai ba da jagoranci ga dukkanin bil Adama a nan duniya, tana kuma yin kira ga gamayyar kasa da kasa da su jaddada alkawarinsu kan gina wata kyakyyawar makoma mai haske ga bil Adama a nan duniya, a lokacin nan na cikon shekaru 70 da kafuwar MDD.
Haka kuma, yayin da Ban Ki-moon ke tsokaci kan matsayin kasar Sin mamba ta MDD, ya bayyana cewa, a matsayin babbar kasa ta biyu wadda take samun bunkasuwar tattalin arziki a duniya, da kuma kasancewar kasar dake kaunar zaman lafiya, kasar Sin ta iya ba da babbar gudummawa ga gamayyar kasa da kasa a fannoni daban daban. (Maryam)