Majalisar dokokin kasar Mozambique ta amince a ranar Laraba da wata doka kan kare kekebbun wuraren namun daji da za ta taimaka wajen yaki da farauta ba bisa doka ba a cikin kasar da kuma taimakawa Mozambique wajen kulawa da arzikin albakatunta cikin dogon lokaci.
Daya daga cikin muhimman makasudin wannan doka da ake son a cimma shi ne na farfado da irin wadannan wurare na kasar domin tabbatar da alfanun muhallin halittu, al'umma da tattalin arziki, in ji ministan harkokin yawon bude ido na kasar Mozambique Carvalho Muaria.
Wannan dokar da ministan yawon bude ido ya gabatarwa majalisar wadda kuma ta samu shiga bisa yawan rinjaye, za ta taimaka wajen yaki da farauta ba bisa doka ba dake janyo raguwar namun daji dake cikin wadannan kebebbun wurare. (Maman Ada)




