in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon shirin raya kasa zai kyautata zaman rayuwar jama'ar kasar Sin
2015-10-29 14:04:22 cri

A yau ne aka kammala taro karo na 5, na kwamitin tsakiyar jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin na 18, taron da ya janyo hankali sosai saboda yadda aka tattauna shirin raya kasa na 13 da kasar Sin ta kan gabatar duk shekaru biyar biyar a wajen taron. Game da wannan sabon shiri, manazartar al'amuran yau da kullum na ganin cewa, zai dora muhimmanci kan kyautata zaman rayuwar jama'ar kasar.

Abin da jama'ar kasar Sin suke fada a nan shi ne, burinsu game da gwamnatinsu, inda suka bayyana fatansu na ganin an kara tallafa wa tsoffin mutane, da shawo kan hauhawar farashin kayayyaki, da kare muhalli, da samar da abinci mai inganci, da kyautata tsarin aikin ilimi da dai sauransu. Duk abubuwan da aka fada sun shafi zaman rayuwar jama'a da bukatunsu na yau da kullum.

A cewar Wang Jun, mataimakin darektan sashin nazarin bayanai na cibiyar musayar bayanan tattalin arziki na kasa da kasa ta kasar Sin, sabon shirin raya kasa da hukumar kasar Sin za ta gabatar a wannan karo zai taimakawa biyan bukatun jama'a.

"Tabbatar da ingancin zaman rayuwar jama'a, da kokarin kyautata shi ya kasance tushen aikinmu, don haka muna dora muhimmanci sosai kan wannan bangare. Dukkan fannonin da jama'a suke da bukata kuma suna maida hankali a kai, kamarsu aikin ilimi, samun guraben aikin yi, albashin ma'aikata, aikin jinya, da dai sauransu, mu ma muna kula da su sosai."

Kafofin watsa labarun kasar Sin sun nuna cewa sabon shirin raya kasar Sin ya kunshi manyan ayyuka guda 10, cikinsu har da kyautata zaman rayuwar jama'a da rage talauci. Wasu masana na hasashen cewa, za a kara kyautata manufofin kasar ta yadda za su amfani jama'a, da ba da karin kulawa ga mutanen dake kauyuka da marasa galihu, ta yadda za a rage gibin dake tsakanin yankuna da mutane daban daban.

Zhu Lijia, wani shehun malami ne a Kwalejin Koyar da Fasahar Mulki ta kasar Sin, ya bayyana cewa don tabbatar da walwalar al'umma, ya kamata a fara da kokarin fitar da jama'ar da suka kai fiye da miliyan 70 daga kangin talauci.

"Ci gaban da jama'a za su iya gani shi ne yadda za a kyautata muhallin wata kasa, da kula da zaman rayuwar jama'a, gami da kokarin kau da talauci. Yanzu a kasar Sin muna da dubun dubatar jama'a da suke fama da talauci. Kula da wadannan mutane zai zama aiki mafi muhimmanci da za mu gudanar a nan gaba. Ba zai yiwu a bar wadannan mutane a baya, a ce an shiga wani zamani na walwala ba."

Burin kasar Sin na kafa al'umma mai walwala zuwa shekarar 2020, yana nufin budewa jama'a damar samun wadata a zaman rayuwarsu. Don cimma wannan buri, dole ne a yi kokarin tabbatar da ci gaban tattalin arzikin kasar. Hasashen da masana suka yi na nuni da cewa, tattalin arzikin kasar zai samu dore kan saurin karuwarsa cikin shekaru 5 masu zuwa, kuma ana sa ran ganin karuwar ba za ta yi kasa da kashi 6.5% ba. A ganin Wei Jianguo, mataimakin shugaban cibiyar musayar bayanan tattalin arziki na kasa da kasa ta kasar Sin, dole ne a samu karuwar tattalin arziki mai karko, sa'an nan za a iya zurfafa gyaran bawul da ake yi a fannoni daban daban.

"Samun karuwar tattalin arziki mai karko zai taimakawa cimma burinmu na zurfafa gyare-gyaren tsarin aikinmu, kamar su kirkiro sabbin fasahohi, da kau da talauci, da gudanar da wasu manyan shirye-shiryen raya kasa."

A cewar masanan kasar Sin, ba za a ce gyare-gyaren da ake yi a kasar Sin sun yi nasara ba, har sai bayan jama'ar kasar sun cimm karin moriya. Ana kuma sa ran ganin jama'ar kasar za su kara jin dadin zaman rayuwarsu, bayan da aka gabatar da sabon shirin raya kasar ta Sin, da kokarin zurfafa gyare-gyaren manufofin gwamnatin kasar, da daidaita hanyar da ake bi wajen raya tattalin arziki, da kyautata hidimar da ake wa jama'a, da inganta tsare-tsaren al'ummar kasar, da tabbatar da kuma manufar kare muhalli. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China