in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An ba da rahoto kan karfin takarar kasashen duniya na shekarar 2015
2015-09-30 16:16:51 cri

An ba da rahoto kan karfin takarar kasashen duniya na shekarar 2015 a yau Laraba a dandalin tattaunawa kan tattalin arziki na duniya, wanda hedkwatarsa dake birnin Geneva. A cikin wannan rahoto, kasar Sin ta rike matsayi na 28 a fannin karfin takara, kuma tana kan gaba a sauran kasashen BRICS, sai dai kasar Switzerland tana ci gaba da daukar matsayi na farko a duniya.

Abokiyar aikimmu Lami ta hada mana bayani kan wannan rahoto.

An tabbatar da matsayin kasashen duniya a rahoton karfin takara ne bisa ma'aunai 12. A wannan shekara, an tantance kasashe da kungiyoyi 140 na duniya a fannin tattalin arzikin su. Kasashe 10 dake kan gaba su ne, kasar Switzerland, wadda ta yi shekaru 7 tana daukar matsayi na farko, kana kasashen Singapore da Amurka sun dauki matsayi na 2 da na 3, daga baya kuma, kasashen Jamus da Holland da Japan da yankin Hongkong na kasar Sin da Finland da Sweden da kuma Ingila suka biyo bayansu.

A fannin jerin sunayen na shiyya-shiyya, nahiyar Asiya na samu bunkasuwa mai kyau. Kasashen Singapore da Japan da yankin Hongkong na kasar Sin sun rike matsayin dake cikin kasashe 10 mafi kan gaba a duniya. Kasar Sin ta dauki matsayi na 28, wanda ya yi daidai da na shekarar bara, tana ci gaba da kasancewa a matsayin farko daga cikin kasashen BRICS.

Rahoton ya ba da shawara cewa, kasar Sin na bukatar yin gyare-gyare kan tattalin arziki domin tabbatar da samun dawamammiyar bunkasuwa, ta yadda za ta daga matsayinta a rahoton. A nahiyar Turai kuwa, kasashen Spain da Italiya da Portugal da kuma Faransa sun kara karfinsu na takara sosai. Kasashen Afrika dake yankin kudu da hamadar Sahara suna cigaba da samun saurin bunkasuwar tattalin arzikinsu kamar shekarun baya, wanda ya kai kusan kashi 5 cikin dari a kowace shekara.

Bugu da kari, rahoton ya ce, ya kamata kasashe daban daban su dauki muhimman matakan yin gyare-gyare kan tsare-tsaren tattalin arziki, da kara karfin samar da kayayyaki da kuma horar da kwararru a dukkan fannoni, ta yadda za a iya ba da tabbaci wajen neman bunkasuwar tattalin arziki da samar da guraban ayyukan yi da kyautata zaman rayuwar jama'a da kuma kara karfin tinkarar kalubale a nan gaba.

An yi bincike a cikin rahoto cewa, kasashe mafi karfin takara sun tinkari rikicin tattalin arziki da samun farfadowa cikin sauri. Amma wassu kasashe ba su iya farfado da tattalin arzikinsu kamar yadda ya kamata ba bayan rikicin tattalin arzikin duniya. Abin da ya sa ake nuna damuwa sosai a kansu, ana ganin cewa, watakila za su shiga cikin halin matsi na tsawon dogon lokaci a yayin da suke fuskantar matsalar tattalin arziki ta nan gaba. Ban da haka kuma, ba da horaswa ga 'yan kwadago da kuma yin amfani da su na da nasaba sosai da karfin takarar wata kasa. Kasashen dake da matsayin kan gaba a rahoton sun gudanar wannan aiki yadda ya kamata. Amma a sauran kasashe da dama na duniya, an rasa damar samun horaswa da tarbiyya masu inganci.

Shugaban zartaswa na dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya Klaus Schwab yana ganin cewa, an haifar da wasu sabbin sana'o'i da tsarin tattalin arziki a sakamakon juyin juya hali na masana'antu a karo na 4 na duniya. Kamata ya yi a dora muhimmanci kan aikin jawo kwararru da kuma kirkiro sabbin kayayyaki.

Ban da haka kuma, dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya ya ruwaito maganar shehun malamin tattalin arziki Xavier Sala-i-Martin na jami'ar Columbia na cewa, raguwar saurin bunkasuwar tattalin arzikin duniya ya zama kalubale ga duk duniya. Don haka ya kamata shugabannin kasashe daban daban su kara daukar matakan yin gyare-gyare da zuba jari ga aikin kirkiro da horar da 'yan kwadago domin tinkarar kalubale.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China