in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta sayi jiragen saman fasinja Boeing guda 300
2015-09-25 13:51:37 cri

An gudanar da bikin sa hannu tsakanin Sin da Amurka ta fuskar kwangilar jiragen saman fasinja a birnin Seattle na kasar Amurka, hukumomi masu ruwa da tsaki na gwamnatin kasar Sin da wasu kamfanoni sun daddale yarjeniyoyi da kamfanin Boeing na kasar Amurka a fannoni daban-daban, ciki hadda hadin kai bisa manyan tsare-tsare, kafa wata cibiyar kamfanin a kasar Sin da sauransu. A sa'i daya kuma, domin biyan bukatun kasar Sin a wannan fanni cikin dogon lokaci, wasu kamfanonin kasar Sin sun sa hannu kan yarjeniyoyi da kamfanin Boeing domin sayen jiragen sama fasinja 300. Wasu masana sun bayyana cewa, wannan mataki ya alamta cewa, Sin da Amurka sun samu sabon ci gaba mai kyau wajen yin hadin gwiwa ta fuskar sufurin jiragen saman fasinja.

A cikin wadannan yajeniyoyin da Sin da Amurka suka daddale, daya daga cikinsu ya fi jawo hankulan mutane, wato yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu wajen kafa wata cibiyar hada jiragen saman fasinja na samfurin Boeing 737, inda bangarorin biyu suka amince da zuba jari cikin hadin kai don kafa wannan kamfani a nan gaba. Wannan shi ne karo na farko da kamfanin Boeing zai kafa reshensa na harhada jiragen sama a ketare.

Babban sakataren kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin Mista Zhang Yansheng ya nuna cewa, wannan aiki ya kasance wani hadin gwiwa bisa babban mataki da kamfanonin kasashen biyu suka yi a fannin jiragen saman fasinja, ya ce

"Hadin kai a tsakanin Sin da Amurka ta fuskar kera manyan jiragen saman fasinja, ya ba da dama mai kyau ga Amurka wajen habaka kasuwar kasar Sin, kuma hakan zai karfafa karfin kamfanonin kasar Sin masu kera jiragen saman fasinja wajen koyon ilmi daga kamfanin Boeing a fannoni daban-daban, abin da kuma zai kawo moriyar juna gare su."

An baiwa sha'anin kera manyan jiragen sama lakabin "Furani masu armashi na masana'antun zamani", saboda ganin yawan sassan inji da ake bukata, ala misali, wani jirgin saman fasinja na Boeing 737 na kunshe da sassan inji fiye da miliyan 50, an iya samar da wani jirgi mai inganci muddin an samar da dukkannin wadannan sassan inji masu inganci. Mista Zhang ya ce.

"Sin ba ma kawai tana fatan samar da muhimman sassan inji na jiragen sama na Boeing ba, har ma tana fatan kera manyan jiragen sama da karfin kanta. Ina da imanin cewa, Sin na da karfinta a wannan fanni, yin hadin gwiwa da kamfanin Boeing na daya daga cikin darusan da Sin za ta koyi da su don fidda fasahar kanta."

Ban da wannan kuma, domin biyan bukatun kasuwar jiragen saman fasinjan kasar Sin cikin dogon lokaci, da sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar hadin gwiwa ta fuskar cinikayya tsakanin kasashen biyu, da habaka hadin gwiwa tsakaninsu ta fuskar masana'antun zirga-zirga a sararin sama. Yayin ziyarar shugaban kasar Sin Xi Jinping a kasar Amurka, kamfanin samar da kayayyakin zirga-zirga a sararin sama na kasar Sin da kuma sauran kamfanoni sun kulla yarjejeniya tare da kamfanin Boeing game da sayen jiragen saman fasinja guda 300 na kamfanin ta Boeing.

Bisa kididdigar da aka bayar an ce, kasuwar jiragen saman fasinja ta kasar Sin ta samun bunkasuwa sosai a shekarun baya, a farkon watannin shida na bana, yawan karuwar riba da kamfanonin zirga-zirgar jiragen saman fasinja masu sayar da hannun jari na kasar Sin suka samu ya kai kashi 700 bisa dari. Ferfasan kwalejin nazarin tattalin arziki da sa ido na jami'ar sha'anin zirga-zirgar jiragen saman fasinja Mista Li Xiaojin ya ce,

"Sakamakon kyautattuwar zaman rayuwar Sinawa, an fi son zaben jiragen sama don tafi yawon shakatawa musamman ma zuwa kasashen ketare. Abin da ya nuna cewa, ana matukar bukatar jiragen sama, kuma an kai ga matsaya daya cewa, kafin shekarar 2050, Sin za ta zama kasuwa ta farko a duniya a fannin zirga-zirgar jiragen saman fasinja, hakan ya sa Sin za ta kai matsayin farko a duniya wajen mallakar jiragen sama. Saboda haka, kasar na da makoma mai kyau a wannan fanni."

Ban da wannan kuma, Mista Li ya ce, wannan ci gaban da aka samu wato sayen jiragen saman fasinja na kamfanin Boeing ya bayyana muhimmin abun dake shafar hadin gwiwa tsakanin Sin da Amurka don kawo moriyar juna. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China