in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a mai da hankali wajen bunkasa tattalin arziki da ingancinta a shirin raya kasa na shekaru 5 karo na 13
2015-10-28 14:31:09 cri

A yayin zama na 5 na zaunannan kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18 da ke gudana a nan birnin Beijing, ana mayar da hankali kan dudduba takardar neman shawara kan shirin shekaru 5 na raya kasa karo na 13, shirin da zai bayyana taswirar neman ci gaban kasar Sin nan da shekaru biyar masu zuwa. Kwararru suna ganin cewa, a shekaru biyar masu zuwa kasar Sin za ta yi kokarin cimma burin kafa zaman al'umma mai wadata a dukkan fannoni, da tabbatar da samun bunkasuwar tattalin arziki, da kuma yin kwaskwarima a wasu muhimman fannoni.

Kwanan baya, wasu kafofin watsa labaru sun bayyana burin da ake son cimmawa a fannoni 10 cikin shirin shekaru 5 na raya kasa karo na 13 na kasar Sin, ciki har da tabbatar da samun bunkasuwar tattalin arziki, da canja hanyar bunkasa tattalin arziki, da kyautata tsarin masana'antu, da inganta yin kirkire-kirkire da dai sauransu. Sai daga cikin batutuwan an fi maida hankali ne kan batun bunkasa tattalin arziki. Game da hakan, mataimakin shugaban cibiyar nazari harkokin tattalin arziki ta kasar Sin Wang Jun ya bayyana cewa,

"A gani na, don daidaita hanyar samun bunkasuwar tattalin arziki, ko kyautata tsarin masana'antu, da farko dai ana bukatar kafa wani muhalli mai kyau na neman ci gaba mai karko, idan ba a iya tabbatar da haka ba, to da kyar ne a iya gudanar da saurn ayyuka na daban. Dole ne a yi kokarin cimma wannan burin ta hanyar da za'a samu bukasuwa."

Bisa shirin, shekaru biyar masu zuwa muhimmin lokaci ne wajen kafa zaman al'umma mai wadata a dukkan fannoni na kasar Sin, ya zuwa shekarar 2020, GDP da matsakaicin kudin shiga na jama'ar kasar za su ninka sau biyu bisa na shekarar 2010. Kwararru sun nuna cewa, idan ana fatan cimma wannan buri, dole ne a tabbatar da samun saurin karuwar tattalin arziki a kalla kasha 6.5 cikin dari. Wang Jun ya ce,

"Akwai bambanci wajen yin kididdiga tsakanin hukumomi daban daban sakamakon yin la'akari da hauhawar farashin kayayyaki. A ganinmu, idan an samu saurin karuwar tattalin arziki daga kasha 6.5 zuwa 7 cikin dari, to za mu iya cimma burin mu."

An yi tsokacin cewa, har yanzu kasar Sin na fuskantar wasu matsaloli wajen samun ci gaba. Game da haka, farfesa na kwalejin harkokin siyasa na kasar Sin Zhu Lijia ya nuna cewa, nazarin yadda za a kawar da matsalolin zai kasance wani muhimmin batu da za a tattauna a cikin shirin, wanda zai shafi yin kwaskwarima a tsarin gwamnati.

"Tabbatar da samun bunkasuwa, da canja hanya, da kyautata tsari, da inganta yin kirkire-kirkire, dukkansu na da nasaba da batun yin kwaskwarima a tsare tsaren gwamnati a nan gaba."

Lokacin shirin shekaru 5 na raya kasa karo na 13, muhimmin lokaci ne ga kasar Sin wajen tabbatar da samun ci gaban tattalin arziki mai inganci. Farfesa Wang Yukai na kwalejin harkokin siyasa na kasar Sin yana mai cewa, ana bukatar zurfafa yin kwaskwarima domin cimma wannan buri.

"Bai dace a canja tsarin bunkasa harkokin kasuwa ba, a yayin da ake kokarin yin kwaskwarima, kamata ya yi a tsaya kan kwaskwarima a fannonin kudi da inganta kasuwar kudin ruwa, da kuma karfafa yin kwaskwarima kan masana'antun karkashin mallakar gwamnati, wadanda za su kasance abubuwan da ake bukata wajen neman bunkasuwa mai inganci a nan gaba."

Abin da kamata ya yi a lura da shi shi ne, watakila karo na farko za a shigar da inganta ra'ayin wayewar kai ta kiyaye muhalli cikin wannan shirin shekaru biyar na raya kasa. An kimanta cewa, a shekaru biyar masu zuwa, kasar Sin za ta shiga wani yanayi na samun saurin bunkasuwa a fannonin sabbin fasahohin watsa labarai, da na halittu, masana'antar da ke samar da na'urorin zamani, sabbin makamashi da kayayyaki, abubuwan hawa masu amfani da sabbin makamashi da dai sauransu. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China