in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharhi: Hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka ba sadaka ko kwace ba ne
2015-10-26 14:35:10 cri

Tun bayan da kasar Sin da nahiyar Afirka suka kaddamar da tsarin dandalin tattaunawa kan hadin kansu a shekarar 2000, ya zuwa yanzu, hadin gwiwar tasu ta shiga wani sabon mataki. An samu gagarumin cigaba bisa ga dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka a bisa manyan tsare-tsare cikin shekaru goma da suka gabata, hadin gwiwar wanda aka kafa ta da zummar cin moriyar juna tsakanin bangarorin biyu. Sannan batun hadin gwiwar bangarorin biyu a fannin tattalin arziki da cinikayya ya yi matukar jan hankulan al'umma.

Amma sakamakon tunani na tsohon yayi da kuma bambancin ra'ayi da ake nunawa, wasu mutane na ganin cewa, Sin ta hada kai tare da Afirka a fannin tattalin arziki da cinikayya ne domin ba da taimako da sadaka, baya ga wasu na ganin cewa, Sin ta yi hakan ne domin kwace albarkatun Afirka kana da mallakar kwasuwannin nahiyar.

Dangane da batun hadin gwiwa tasakanin Sin da kasashen Afrika, idan da ya kasance bangare daya ne ke samun cin moriya, yayin da daya bangaren ke tafka hasara, to hakika da wannan hadin gwaiwa ba zai ci gaba da kasancewa ba, balle ma a yi batun samun ci gaba. A cikin shekaru 15 da suka gabata, hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin tattalin arziki da cinikayya ta samu saurin bunkasuwa. Alal misali, jimillar cinikayya a tsakaninsu ta zarce kudin Amurka Dala biliyan 222 a bara, yayin da adadin jarin da Sin ta zuba a nahiyar Afirka ya zarce Dala biliyan 30, wadanda suka ninka sau 22 da kuma sau 60 bisa na shekara ta 2000. Hakan ya bayyana karara cewar, hadin kan bangarorin biyu a wadannan fannoni ya kawo wa juna moriya.

Hakika, kasar Sin ta dukufa kan raya ayyukan tattalin arziki da cinikayya tsakanin ta da Afirka ba wai don ba da sadaka ko taimako kawai ba. Yanzu haka, dangantaka a tsakanin Sin da Afirka ta shafi cinikayya da zuba jari da ayyukan kwangila da dai sauransu, ba wai aikin tallafi kawai ba. Kawo yanzu dai, kasar Sin ta kasance abokiyar Afirka mafi girma wajen cinikayya, Afirka kuwa ta zama muhimmin wurin samar da danyen kayayyaki ga Sin, da kasuwa ta biyu a duniya da Sin ke gudanar da ayyukan kwangila, baya ga wuri mafi muhimmanci na hudu da Sin ta zuba jarinta.

A 'yan shekarun nan, Sin da Afirka sun fi ba da muhimmanci kan hadin kan masana'antu. sannan taron koli na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afirka wato FOCAC wanda za'a gudanar a kasar Afirka ta Kudu a farkon watan Disambar bana zai sa kaimi ga ingantuwar dangantaka a tsakanin bangarorin biyu daga dukkan fannoni, ciki har da sauya fasalin tsarin cinikayyar kayayyaki tsakaninsu ya zuwa ga hadin kan masana'antu da musayar fasahohi.

Kasancewar kasar Sin ta kaddamar da wani sabon tsarin yau da kullum kan tattalin arzikinta, don haka wasu matsaloli kan masana'antu suna ta bullowa. Lokaci ya yi da Sin zata maida wasu daga cikin masana'antunta da ke bukatar yawan 'yan kwadago kamar su siminti, karfe, gilas zuwa kasashen ketare. A bangare guda, sakamakon irin bukatun da Afrika ke da shi a wadannan fannoni da kuma albarkatunta na halittu da na kwadago, gami da kyakkyawan muhallin kasuwanci, ya sa ala tilas ta zama wurin da ya fi dacewa da a fara raya masana'antun kere-kere.

Kasashen Afirka da dama na dokin amfana daga wannan kyakkyawar damar inganta yanayin tattalin arzikin na Sin ta yadda su ma za su amfana wajen raya masana'antu. Har ma wasu 'yan Afirka sun yi amanna cewar, kasar Sin ta ci gajiya sosai ta fuskar raya masana'antu da ke bukatar yawan kwadago yayin da kasashe masu sukuni suka canja salon tattalin arzikinsu sama da shekaru 30 da suka gabata, don haka yanzu ya kamata Afirka ita ma ta kama wannan kyakkyawar dama don raya masana'antu na kansu.

Hakan ana iya ganin cewa, kasar Sin ta tallafa wa Afirka wajen raya masana'antu, ba ma kawai wannan zai kawo alheri ga Afirka ba, hatta ma zai taimaka mata wajen kyauatata tsarin tattalin arzikinta, don haka wannan babban aiki a tsakanin Sin da Afirka zai kawo moriya ga dukkan bangarorin biyu.

Haka zakila, ba kamar yadda wasu 'yan siyasa da kafofin watsa labaru suka cewa, wai Sin ta hada gwiwa tare da Afirka ne domin kwace tattalin arzikinta kawai.

A halin yanzu, kasashe daban daban na Afirka na sa ran ganin gaggauta ci gaban masana'antunsu da raya ayyukan noma na zamani, a kokarin samun dauwamammen ci gaba bisa dogaro da kansu. Hadin kan Sin da Afirka a fannin tattalin arziki da cinikayya ya karya lagon rashin adalci da kasashen yammacin duniya suka tsara, wanda kuma zai ba da taimako ga Afirka wajen samun 'yancin kan tattalin arzikinsu. Don haka irin hadin kai a tsakanin bangarorin biyu zai kara azama ga tattalin arzikin duniya wajen samun daidaito da kara hakuri da juna gami da samun ci gaba mai dorewa, wanda na da babbar ma'ana sosai.

Bugu da kari, kasar Sin ta nanata cewa, yayin da take taimaka wa Afirka wajen raya masana'antu, ta alkawarta magance bin tsohuwar hanyar mulkin mallaka da wasu kasashen yammacin duniya suka bi, haka kuma ba za ta gurbata muhallin hallitun Afirka da kawo illa ga moriyarta cikin dogon lokaci ba.

Wani abin da ya kamata mu lura ko da yaushe shi ne hadin kan Sin da Afirka a fannin tattalin arziki da cinikayya ya kan bi ka'idojin bude kofa ga juna da yin hakuri da juna. A bana, Sin da Faransa sun cimma daidaito kan hadin gwiwarsu a Afirka, baya ga Sin da Amurka suka amince da inganta hadin kansu da Afirka nan ba da jimawa ba. Duk wadannan abubuwa sun sheda cewa, kasar Sin na da aniyar hadin gwiwa tare da ko wane bangare a Afirka bisa ka'idojin "sanya bangaren Afirka ya gabatar da shiri, da amince da shirin, yayin da ba da jagoranci ga shirin", ta yadda za a iya kiyaye babbar moriyar Afirka yadda ya kamata.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China