Mista Luis Segura ya ce ana bukatar samun goyon baya daga kowa da kowa, domin in ba haka ba shugabannin hukumarsa ba za su samu damar daidaita matsalar ba, ko da yake za su yi iyakacin kokarinsu.
Mista Luis ya fadi haka ne yayin da ya yi hira da jaridar Perfil ta kasar Argentina, inda ya ce dalilin da ya sa ake ta samun tashin hankali a yayin wasanni a kasar, musamman ma a kwanakin nan shi ne, domin al'adun al'ummar kasar na son nuna karfin tuwo. A cewarsa, yanayi ya riga ya zama ba wanda zai iya kula da shi, ganin yadda masu kallon wasa za su iya shiga filin wasa, su jifi 'yan wasa da duwatsu. Ya kara da cewa, za a samu damar daidaita wannan matsala, bayan da aka samu tsaro, da manufofi masu inganci, da adalci, gami da shugabanni masu sanin kima a kasar.(Bello Wang)