Zidane, wanda ke aiki a matsayin babban koci na Castilla, kungiyar matasa ta Real Madrid, ya ce PSG da Real Madrid su ne kuloflika guda biyu da suka fi yiwuwar cin nasara a gasar zakarun Turai ta wannan kakar wasa.
Zidane ya fadi haka ne yayin da yake hira da wata tashar gidan telabijin ta kasar Faransa, inda ya ce 'yan wasan PSG sun san tsarin gasar Faransa sosai, har ma karfinsu ya wuce na dukkan kuloflika kasar Faransa.
Sai dai ko da yake PSG ya lashe kambin gasar Ligue 1 a kakar wasa guda 3 a jere, hakika a duk wadannan shekaru 3 kulof din ya na komawa baya ne a zagayen kusa da na karshe wato "quarterfinal" a Turance, tun bayan da ya koma gasar zakarun Turai a shekarar 2012.
A kakar wasan da muke ciki, PSG ta ci nasara a wasannin 2 da suka gudana tsakanin rukunin A, inda ya lashe Malmo, da Shakhtar Donetsk, amma a zagaye mai zuwa zai kara da Real Madrid cikin wasanni 2.(Bello Wang)