Ban da haka, lauyan mista Blatter Richard Cullen ya bayyana a cikin wata sanarwa cewar, Blatter ya jaddada cewa bai taba karya doka ba, kana kudin da ya ba Michel Platini, shugaban hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafa ta nahiyar Turai, wanda ya kai Swiss Franc miliyan 2, kudi ne da ya dace da doka, kuma hakan bai keta ka'idojin hukumar FIFA ba.
Kafin haka kuma, hukumar binciken laifi ta kasar Switzerland ta sanar a ranar 25 ga watan nan cewa, ta kaddamar da bincike kan mista Sepp Blatter, bisa zargin da aka yi masa na cin kudin hukumar FIFA da sakaci da aikinsa. An ce Blatter ya taba biya ma shugaban kungiyar wasan kwallon kafa ta nahiyar Turai Michel Platini kudin hanci. Amma a cewar mista Platini, ya karbi kudin ne a matsayin albashi, ganin yadda ya taba aiki a matsayin mai ba da shawara ga Blatter tsakanin shekarar 1999 da ta 2002.(Bello Wang)