Shugaban hukumar na yanzu Sepp Blatter, da Michel Platini na cikin wadanda suka samu halartar wannan taron, inda aka amince da cewa dukkanin masu nufin shiga takara a zaben, su sanar da burin na su kafin ranar 26 ga watan Oktombar dake tafe, lokacin da ake sa ran bayyanar 'yan takara 5.
Baya ga tabbatar da lokacin zaben, taron ya kuma tattauna kan wasu matakai da hukumar za ta dauka na farfado da kwarjinin ta, ta hanyar gudanar da kwaskwarima, ciki hadda kayyade wa'adin shugabancin jagoran ta.
An dai tabbatar da lokacin zaben shugaban hukumar, wanda hakan ya bayyana cewa watanni 7 ya rage cikin wa'adin aikin shugaban ta na yanzu wato Sepp Blatter, wanda aka bayyana cewa mai yiwuwa ya janye shawarar da ya yanke ta yin murabus. Idan hakan ta tabbata, Sepp Blatter zai ci gaba da jagorantar FIFA ke nan zuwa watan na Fabarairu, lokacin da za a zabi sabbin shugabannin hukumar. A kuma kasance jagoran hukumar ne tun cikin shekarar 1998.
A baya dai muhimman 'yan takarar da suka bayyana burinsu na shiga zaben, sun hadda da tauraron dan wasan kwallon kafa na kasar Brazil Arthur Antunes Zico, da shugaban kungiyar kwallon kafa ta kasar Laberiya Musa Bility. Sai kuma shugaban kungiyar kwallon kafar turai Michel Platini, da Yarima Ali Bin Al-Hussein wanda Platini ya doke a zaben shugabancin FIFAr da ya gudana a karshen watan Mayun bana. Wadannan mutane biyu dai na sahun gaba a neman wannan mukami.(Amina/Saminu)